Yunwa na addabar 'yan Afrika ta Tsakiya

Image caption Rikici ya addabi al'ummar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

Hukumar samar da abinci ta duniya WFP, ta ce rabin al'ummar Jamhuriyar Tsakiyar Afrika na fama da matsalar yunwa sakamakon rikicin da kasar ke fama da shi.

A cewar wani rahoton da hukumar ta fitar, kusan mutane miliyan biyu da rabi ba su da damar samun abinci, adadin da ya ninka yawan wadanda suka sha fama da matsalar yunwa shekara daya da ta gabata.

Hukumar WFP ta ce farashin kayayyakin abinci ya ci gaba da tashi sakamakon rashin albarkar amfanin gona.

Wannan al'amari ne ya tilasta dubun-dubatar mutane watsar da harkar noma.

An shafe kimanin shekaru uku ana tafka rikici a kasar, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da raba mutane da muhallansu.