Dangote da Bill Gates za su tallafa wa yaki da Maleriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Maleriya wadda sauro ke yadawa, na daga cikin cututtukan da ke addabar 'yan Najeriya.

A Najeriya an sake sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin wasu gwamnatocin arewacin kasar da kuma gidauniyar Dangote da ta attajirin nan mai kamfanin Microsoft, Bill Gates.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne domin yaki da zazzabin cizon Sauro da kuma ci gaba da yaki da cutar shan Inna.

Gwamnonin jihohin Borno da Yobe da Kano da Sokoto da kuma Kaduna ne suka sanya hannu a yarjejeniyar.

Wasu sarakunan gargajiya na yankin ma sun halarci taron wanda aka yi shi a ranar Laraba, a Kaduna.

Cutar shan Inna da zazzabin cizon sauro na daga cikin cututtukan da suka addabi Najeriya musamman ma arewacin kasar, kuma sun hallaka mutane da dama.

Sai dai a baya-bayan nan hukumomi sun ce an samu nasarar kawar da cutar shan Inna.