Olubadan ya mutu

Image caption Olubadan ya mutu ne yana da shekara 101 a duniya.

Babban Basaraken nan na Ibadan, Oba Samuela Odulana Odugade, ya mutu.

Oba Odugade ya mutu ne ranar Talata, kuma a yau ne ake sa ran fitar da sanarwar mutuwar a hukumance.

A cewar wata majiya daga masarautar, Basaraken ya mutu yana da shekaru 101.

Mamacin ya yi bikin cika shakera 100 a shekarar 2014 kuma da a ce yana da rai, a shekarar nan ne zai cika shekara 102.

Sarautar Olubadan na nufin "Ubangijin Ibadan" kuma shi ne babban Basaraken Ibadan.

Duk da ya ke a yanzu Olubadan ba shi da karfi irin na gwamnati, amma yana taka muhimmiyar rawa a kan al'amuran da suka shafi yankin kudu maso yammacin Najeriya.