'Yan bindiga sun kai hari a jami'ar Pakistan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'ai sun ce mutane 19 ne suka mutu a harin.

Hukumomi a Pakistan sun ce ya zuwa yanzu mutane 19 ne suka mutu bayan 'yan bindiga sun kaddamar da munanan hare-hare a wata jami'a da ke kasar.

Rundunar sojin kasar ta ce an daina jin karar harbe-harbe a jami'ar ta Bacha Khan, mai dalibai 3000 da ke gundumar Charsadda da ke arewa maso yammacin kasar, bayan sao'i uku.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani Farfesa masanin kimiyyar sinadarai ya rasa ran sa, wasu mutane 50 kuma sun ji rauni.

Sai dai sojin sun ce suna ci gaba da yin bincike domin gano ko akwai ragowar 'yan bindigar a cikin jami'ar.

'Yan sanda sun ce an kashe akalla 'yan bidigar hudu, ko da ya ke ba a sani ba ko wasu sun tsere.

A shekarar 2014 ma, 'yan kungiyar Taliban sun kashe dalibai 130 a birnin Peshawar da ke kusa da Charsadda.