Rasha za ta rage kudin binciken sararin samaniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Rasha ta sanar cewar za ta zaftare yawan kudaden da ta ke kashewa a harkar binciken sararin samaniya.

Wannan na faruwa ne yayin da kasar ke shirye shiryen daukar matakan tsuke bakin aljihu domin magance asarar da dauwar farashin mai ke haifar mata.

Wakiliyar BBC ta ce "za'a rage kasafin kudin binciken sararin samaniyar zuwa kashi 30 cikin 100.

Ta kara da cewar za a jinkirta shirin tura 'yan sama - jannati na farko 'yan Rashan zuwa duniyar wata zuwa a kalla shekaru biyar, inda yanzu aka mai da shi har zuwa shekarar 2035".