Bam ya hallaka mutane shida a Masar

Jami'an tsaro a Masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan IS na kai hare-hare kan jami'an tsaro.

Wani bam da ya tashi a birnin Alkhaira na kasar Masar, ya hallaka mutane shida ciki har da 'yan sanda uku.

Majiyar jami'an tsaro ta rawaito cewa bam din ya tashi ne a lokacin da 'yan sanda suka kai samame wani gida da ake kyautata zaton maboyar masu tada kayar baya ne da ke makwaftaka da Dalar Pyramid.

Mayakan IS sun zafafa kai hare-hare akan Sojoji da 'yan sanda a kasar, tun bayan hambarar da gwamnati shugaba Muhammad Morsi na jam'iyyar 'yan uwa musulmi a shekarar 2013.