Boko Haram ta lalata rijiyoyi a Borno

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima
Image caption Rikicin na Boko Haram ya lalata garuruwan jihar Borno.

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa-maso-gabashin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram sun lalata kusan daukacin wuraren samun ruwan sha a dukkannin yankunan kananan hukumomi 22 da aka kwato daga hannunsu, a watannin baya-bayan nan.

Kwamishinar Ruwa a jihar Dakta Zainab Gimba ta shaida wa BBC cewa, wannan ya sa 'yan gudun hijirar ke komawa garuruwansu na asali ba su da hanyoyin samun ruwan sha.

Ta kara da cewa babu wata hanyar samun ruwan sha a cikinsu, a daukacin kananan hukumomin da suka kai ziyarar gani da ido.

A cewarta, gwamnatin jihar Borno ta dauki matakin sake tona rijiyoyin burtsatsai a wadannan garuruwa.