Tamowa: Gates da Dangote za su kashe miliyoyi

Hakkin mallakar hoto US Embassy Nigeria
Image caption Galibin taimakon zai kasance ne a arewacin Najeriya

Gidauniyar Bill and Malinda Gates da kuma ta Dangote Foundation sun saka hannu kan wata yarjejeniyar na bayar da dala miliyan 100 domin yaki da matsalar tamowa tsakanin kananan yara a Najeriya.

Shugabanin cibiyoyin biyu watau Bill Gates da kuma Alhaji Aliko Dangote ne suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar a wani takaitaccen biki a Abuja babban birnin Najeriya.

A yayin yarjejeniyar manyan attajiran biyu a duniya, sun amince da kashe wadannan makudan kudin ne kan yara masu tamowa a Najeriya daga nan zuwa shekara ta 2020.

A cewar Shugaban gidauniyar Dangote , Alhaji Aliko Dangote, sun yanke shawarar fadada ayyukan su na bayar da agaji zuwa wannan fannin ne bayan gano cewa matsalar ta tamowa ita ce kalubale mafi girma da ke yin tarnaki ga kokarin suka jima suna yi na rage mutuwar kananan yara a kasar.

Alkalumman hukuma a kasar sun nuna cewa matsalar ta tamowa ta fi kamari a shiyoyin arewa maso gasa da arewa maso yamma musamman a jihohin Kano da Katsina da Kaduna da Jigawa da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi.

Sai kuma jihohin Taraba da Adamawa da Borno da Yobe da Bauchi da kuma Gombe a arewa ta gabas.

A jawabinsa Ministan Lafiya na kasar, Farfesa Isaac Adewale ya ce a halin yanzu kimanin kashi 10 cikin 100 na jama'ar kasar ne ke fama da matsalar ta tamowa.