Ana binciken zoben aure a cikin bola

Zoben alkawari na Aure Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sanya zoben alkawari na Aure dai wani abu ne mai muhimmanci ga mata Yahudawa.

A kasar Isra'ila, masu aikin agaji irin na sa-kai, wanda 'yan magana kan ce ya fi bauta ciwo sun kai dauki ga wata Bayahudiya, wadda bisa rashin sani zobenta na alkawarin aure ya fada cikin shara ko bola.

Matar ba ta ankara ba sai da motar kwasar shara ta tafi da kunshin bolar da zoben nata ya fada ciki, kodayake daga baya an bi motar an tsayar da ita.

Daga nan sai aka umurci direban ya juye shara a wani wuri da masu agaji suka dukufa wajen baje tsibin bolar, suna neman zoben.

Sun dai sha alwashin ci gaba da nema har sai sun samun zoben alkawarin.