'Yar Nigeria na horas da 'yan ci-ranin Afghanistan

Image caption Perpetua Nkwocha ta shafe shekaru bakwai a Skellefte

Fitacciyar ‘yar wasan kwallon kafa ta Najeriya Perpetua Nkwocha, ta samu kanta a wani waje nesa da kasarta, ta kuma fara sabuwar rayuwa.

Aikinta ya dauke ta daga Najeriya zuwa China inda daga can kuma ta samu kanta a kasar Sweden, inda take zaune a garin Skelleftea a arewacin kasar fiye da shekaru bakwai.

A yanzu dai, ‘yar wasan wadda ta taba zama gwarzuwar ‘yar kwallon Afrika har sau biyu, tana taimakawa sauran mutane da suma suka bar kasashensu ta kuma hadu da su a kasar Sweden.

Tana horas da wata tawagar kwallon kafa a garin, amma a wannan hunturun na bana ta mayar da hankali ne wajen horas da wata tawaga ta matasa ‘yan Afghanistan, wadanda ke cikin daruruwan ‘yan ci-ranin da

suka isa garin a watannin baya-bayan nan.

Ta shaidawa BBC cewa, “Na ga kamar tafiyarmu daya ne ni da su, shi yasa na yi ta kokarin sanya su farin ciki, saboda na san daga inda suka fito.”

“Muna kokarin yi musu kyakkyawar maraba da sanya su farin ciki da kuma hada su abota da mutane ‘yan ainihin kasar Sweden,” in ji Perpetua.

“Matashi Habibullah dan Afghanistan”

Wani matashi dan Afghanistan mai suna Habibullah y ace, “Gaskiya kwararriyar mai horas da mutane ce, kamar yadda ka ke gani akwai mutane da dama da ke wasan kwallo a nan kuma suna jin dadi. Dukkan mu muna jin dadin aiki da ita.”

Kulob dinta na Clemensnas IF tare da hadin gwiwar wata kungiyar kwallon kafa ta garin da kuma wani coci sune suka kirkiro da wannan aikin, wanda aka fara shi tun a watan Nuwamba.

Shugaban kulob din Clemensnas IF Jens Karlsson, y ace, “An kirkiri wannan aiki ne domin a samarwa matasa abin debe kewa a tsawon yini. Idan suna kaunar kwallon kafa, to suna iya zuwa nan su koya a wajen

Perpetua domin kwararriyar ‘yar kwallo ce.”

Wadannan matasa dai, wadanda yawancinsu sun taho ci-rani ne daga Afghanistan a karan kansu, suna matukar jin dadin wasa karkashin sa idon kociyar tasu Perpetua.

Sai dai zai yi wuya ma idan sun san irin rawar da ta taka da kuma nasarorin da ta samu a harkar kwallon kafa, amma ko da basu sani ba, to hakika sun shaida hakan ta irin salon da take basu horo.

“Kalubalen ci-rani”

Kamar dai yadda aka sani batun ci-rani wani al’amari ne mai cike da rudani a Sweden da ma nahiyar Turai baki daya, amma hukumomi a garin Skelleftea, wadanda ke goyon bayan aikin kungiyar kwallon kafa ta

Clemensnas sun nuna matukar bukatarsu ta ganin baki na zuwa garinsu don su samu cikar burinsu na yin rayuwa mai kyau.

Wani Kansila a garin mai suna Daniel Adin, ya shaida wa BBC cewa, “Muna da matsala ta wajen zirga-zirgar mutane musamman idan suna son shiga manyan garuruwa da ke kudancin kasar.”

Mista Adin dai na cike da muradin ganin an yi amfani da wannan damar ta wasan kwallo don karbar bakuncin baki masu son zuwa garin.

Perpetua dai ta ce tana jin dadin rayuwarta a Skelleftea domin mutanen garin na da karamci, matalarta daya matsanancin sanyin da ake zugawa.

“Gaskiya sanyin ya yi yawa, ba dama fa ka yi wani gayu lokacin hunturu,” a cewar Perpetua.

Tana da ayyuka da dama da take yi baya ga horas da wasan kwallo, tana zuwa makaranta domin koyon yaren kasar wato Swedish.

Babban aikin da za ta yi nan gaba shi ne a watan Mayu za ta jagoranci kungiyar Clemensnas don ganin ta kai ga ci.

Perpetua ta ce tana matukar jin dadin kasancewa da wadannan matasa domin tana jin kamar a gida Najeriya take lokacin da take horas da yaranta a can.