'Yan Gamborou sun fara komawa gida

'Yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption 'Yan gudun hijirar sun fara komawa gida.

Rahotanni daga Nigeria na cewa wasu daga cikin 'yan gudun hijirar garin Gamboru da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru sun fara komawa gidajensu.

Mutanen sun tsere ne a 2014 bayan da mayakan Boko Haram suka mamaye garin suka karkashe jama'a da dama tare da kona gidaje, da dukiya mai dimbin yawa.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallansu a Najeriya musamman a jihar Borno.

Tashin hankalin wanda aka shafe shekaru shida ana yi, ya janyo mutuwar mutane fiye da 18,000.

Daga London Ahmad Abba Abdullahi ya tuntubi wani mutum mai suna Malam Ali, wanda yana daya daga cikin wadanda suka koma, ga kuma yadda hirar ta kasance