An samu raguwar makanta a Nigeria

Wasu Makafi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matsalar Makanta ta ragu a Nigeria.

Masana kimiyya sun ce sun yi wani gagarumin yunkuri wajen yin allurar riga-kafin makanta wadda kudan bakin-kogi ke haddasawa.

Masanan dai sun gano wasu sinadarai uku da za a yi amfani da su wajen hada allurar riga-kafin cutar makantar, wadda ke kama kimanin mutum miliyon goma sha bakwai a kowace shekara.

Masana sun ce kashi casa'in cikin dari na masu kamuwa da cutar na fitowa ne daga nahiyar Afirka.

Sai dai kuma Dr Ibrahim Kana, wani kwararren likitan Ido a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa an samu raguwa matuka a yawan wadanda suka kamu da cutar Makanta sanadiyyar cizon kudan bakin-kogi a Najeriya.