Tattalin arzikin duniya na tangal-tangal

Hannayen jarin Amurka Hakkin mallakar hoto
Image caption Faduwar farshin danyan mai a kasuwar duniya ya taimaka wajen sanya tattalin arziki shiga halin ni 'ya su.

An tabka asarar biliyoyin dala a kasuwannin hada-hadar hannayen jari a sassa daban-daban na duniya sakamakon damuwar da aka shiga saboda faduwar farashin mai da kuma fargabar da ake yi cewa tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya.

A New York, kasuwar hannun jari ta Daw Jones ta yi faduwar kashi daya da rabi bisa dari, kuma a hakan ma ta farfado ne daga mummunar faduwar da ta yi a baya.

Kazalika, kasuwannin hannayen jari na Nasdaq da Standard and Poor duka sun yi faduwar da ba su taba yin irin ta ba a cikin watanni 15 din da suka wuce.

A Turai ma asarar aka tabka, saboda farashin hannun jarin ya yi faduwar da bai taba yin irin ta ba a cikin watanni goma sha biyar din da suka wuce.