Ruwa ya ci mutane 40 a tekun Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu aikin ceto ne kokarin kubutar da mutane a tekun

'Yan gudun hijira fiye da 40 ne ake san cewar ruwa ya ci a lamura biyu daban daban a gabar tekun Turkiya.

Hakan na faruwa ne a yayin da dubban 'yan ci-rani ke ci gaba da kama hanyar zuwa Tarayyar Turai.

Jiragen ruwa biyu sun nutse a cikin ruwa mai sanyi a kusa da tsibirin Girka.

Gwamnatocin Jamus da Turkiyya na gudanar da taron majalisar ministocin hadin gwiwa a Berlin kan matsalar 'yan gudun hijirar.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, na san Turkiyya ta tsaurara sa ido a kan iyakokinta, ita kuma za a bata kudi da ma wasu alfarma.

A halin da ake ciki kuma Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce Amurka za ta nemi taimako domin kara kudaden bayar da gudumawar jin kai na shekara shekara a ko'ina cikin duniya da kashi 30 cikin dari ya zuwa jimillar dala biliyan 13.