Murdoch: Manhajar tsaron GCHQ na da rauni

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption GCHQ Surveilance

Wani masani a kan harkokin tsaro a jami'ar London, wato University College, Steven Murdoch ya ce manhajar da ke hana tatsar wayar ta hukumar leken asirin Birtaniya, GCHQ na da rauni.

Mista Murdoch ya bayyana hakan ne a cikin wani sakamakon binciken da ya gudanar, yana cewa manhajar tana da rauni saboda tana ba wa hukumar damar tatsar bayanan wayoyin jama'a.

Ya ce kamata ya yi manhajar ta hana wasu tatsar bayanan da ake yi ta wayoyin hukumar kadai, saboda haka damar da ta ke ba wa jami'an hukumar suna sauraron hirarrakun da jama'a ke yi kutse ne ga sirrin jama'a, don haka ana shiga hakkinsu.

Sai dai hukumar leken asirin Birtaniya a nata bangaren ta ce ba ta amince da wannan sakamakon binciken ba.

Babbar damuwar Mista Murdoch ita ce yanda aka tsara manhajar ta kasance wani ka iya kutse cikin wayar da mutum biyu ke yi, saboda a nasa ra'ayin kamata ya yi a ce babu wata kafa da wani zai iya shiga tsakanin mutane biyu idan suna magana ta waya.

Ya shaida wa BBC cewa tun da an kafa hukumar ne don hana masu kutsen wayar jama'a aika-aikarsu, to, bai kamata mai dokar barci ya buge da gyangyadi ba.

Har yanzu dai ana ci gaba da takaddama a kan hanyoyin da ya kamata hukumomin Birtaniya su dinga bi wajen yin kutse cikin bayanan jama'a, wato iyakokin da ya kamata su tsaya da kuma irin damar da ma'aikatun gwamnati za su ba wa jama'a wajen samun bayanan da suka shafe su.