Sankarau ya kashe mutane 27 a Ghana

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomin lafiya a kasar Ghana sun ce cutar sankarau, wacce ta barke a jihar Brong Ahafo, ta kashe akalla mutane 27

Hukumar yaki da bazuwar cututukar kasar dai ta ce mutane sama da 90 ne suka kamu da cutar.

Sai dai ta kara da cewa tana iya kokarinta don ganin an shawo kan cutar da ke ci gaba da yaduwa zuwa wasu jihohin kasar.

Yanayin zafi da cunkoson jama'a ne dai manyan abubuwan da ke haddasa cutar.