Aston Villa na cikin rikici — Hollis

Image caption Steve Hollis ya ce akwa matsala a Aston Villa

Sabon kociyan Aston Villa, , ya ce kungiyar tana cikin mummunan rikicin da ta shafe a kalla shekara goma ba ta samu kanta a cikinsa ba.

Kungiyar dai tana can kasa a teburin Firimiyar Ingila inda ta tsira da maki goma.

Hollis ya shaida wa BBC cewa, "A wasan kwallo, hakan ba karamar fitina ba ce, wannan ne mataki mafi muni da kungiyar ta samu kanta a ciki shekaru da dama da suka gabata."

Hollis ya kara da cewa littafin jerin sunayen 'yan wasa a bude yake idan har ana son sayen sabbin 'yan wasa.