An kai hari Babban Gida a jihar Yobe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Babban Gida dake karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe na cewa wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari cikin dare a garin, inda suka yi ta harbe harbe da kuma kona wani wuri.

Wasu mazauna garin sun ce da misalin karfe daya da rabi na dare ne maharan suka diran ma garin, lokacin mutane na barci.

Sai dai saboda yanayi na dare, ba tantance ko an rasa rai a harin ba, da kuma irin barnar da 'ya kungiyar suka hadda sa.