An kashe mutane uku a makaranta a Canada

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Makarantar La Loche Community

'Yan sanda a Canada sun ce an kashe mutane 4 a lokacin da wani mutun ya bude wuta a wata makaranta a lardin Saskatchewan (Sas-ka-ce-wan) dake tsakiyar kasar.

Rahotannin da aka bayar daga farko, sun nuna mutane biyar ne suka mutu a harin.

An kama wani mutun guda da ake zargi, a wajen makarantar La Loche Community, inda aka bude wutar.

Firayiministan kasar Justin Trudeau ya yi allawadai da harin.

Ya bayyana harin a matsayin wani mummunan mafarki da iyayen yara za su suyi.

'Yan sanda a kasar kuma, su na binciken wani al'amarin bude wutar na biyu da aka samu a cikin wata al'umma mai mutane dubu uku.

Ba kasafai dai ake samun irin wannan harbe harbe a Canada ba, inda dokokin mallakar bindiga suke da tsaurin gaske, fiye da Amurka.