Google zai biya Burtaniya harajin $200m

Hakkin mallakar hoto

Katafaren kamfanin fasaha na Google ya amince ya biya Burtaniya kusan dala miliyan 200 a matsayin harajin da ya zamewa biya na shekaru 10 da suka gabata.

Ana zargin kamfanin na Google da zamewa biyan haraji, duk da cewa yana samun biliyoyin dala a hada-hadarsa a Burtaniya.

Masu suka dai na ganin kudin da kamfanin ya ce zai biya yanzu, sun yi kadan.

Sai dai Google din ya ce ya kimanta kudin ne da irin girman kasuwancinsa a kasar, sannan ya sha alwashin biyan karin haraji nan gaba.

Kamfanin na Google ya na cikin kamfanonin fasaha da suka gamu bincike saboda zargin yin kumbiya-kumbiya wajen biyan haraji.