Barayin shanu sun koma fashi a Kaduna

Image caption Wasu barayin shanu da aka kama a Kaduna

A Najeriya, wasu al'ummomin kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari a jihar Kaduna sun koka da sabon salon fashi da makami da garkuwa da mutane, da kashe-kashe a yankunan su.

A cikin wata takarda da suka aikewa gwamnatin jihar Kaduna, al'ummomin sun ce barayin shanu da wasu bata gari da aka kora daga dajin Kamuku, sune suke addabar mutane a cikin gari.

Dajin Kamuku wanda ya hade da jihohin Kaduna da Zamfara, da Naija da kuma Katsina, ya yi kaurin suna wajen zama matattarar barayin shanu da 'yan ta'adda.

Sojoji sun fatattaki bata garin daga cikin dajin, lamarin da yasa suka koma cikin gari da wani sabon salo.

Al'ummomoin Giwa da Birnin Gwari sun bukaci gwamnati da ta kara kaimi na kawar da bata garin domin raba jama'a da sabbin matsalolin da suka taso.

Daya daga cikin mutanen Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Abdulra'uf ya ce masu satar shanu su na tare hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, da kuma hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua a kowacce rana.

Ya ce bata garin suna karbe wa mutane kudi, sannan su sace mata domin karbar kudin fansa ko kuma cin zarafin su.

Wani danmajalisar wakilai daga yankin, Hassan Adamu Shekaru ya ce a kwanakin baya an sace Dagacin Takama a Birnin Gwari, sannan aka kashe Dagacin Kadage a Giwa, kuma ana ci gaba da sace mutane.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta na sane da matsalar kuma ana daukan mataki na hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro don magance matsalar.

Brayin shanu sun dade suna cin karen su ba babbaka a dajin Kamuku, lamarin da yasa noma ya yi wa muatne wuya.