Amurka ta damu da tasirin Iran a Lebanon

Hakkin mallakar hoto AFP

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya baiyana damuwa a kan irin rawar da Iran ke takawa a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Da yake jawabi bayan wata tattaunawa a Saudiyya, Mr Kerry ya yi nuni kan goyon bayan da Iran ke baiwa yan Hizbullah a Lebanon wadanda ke marawa shugaba Assad baya a yakin basasar Syria.

Ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubair yace kasarsa na aiki da Amurka domin kawar da abin da ya kira barazanar da Iran ke yi.