Kankara ta halaka mutane 18 a Amurka

Image caption Dusar kankara ta kara ta'azzara a Amurka

An dage wani hanin tafiye tafiye da aka saka a New York a lokacin matsanancin hunturun da yayi kaca - kaca da gabacin Amurka.

Direbobi sun fuskanci tara da ma kamu idan suka saba wa hanin.

Sai dai kuma Magajin garin birnin, Bill de Blasio, ya bukaci mutane da su kaucewa tafiye tafiyen babu gaira ba sabar, su yi zamansu a gida.

An danganta matsanancin yanayi -- wanda ya haddasa zubar kankara mai tudun mita daya -- da mutuwar mutane akalla 18.

Dubun dubatar mutane sun kasance babu wutar lantarki , sannan ana sa ran jiragen sama kalilan su tashi daga New York ko kuma Washington a yau.