Ghani ya yi gargadi kan Taliban

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ashraf Ghani ya yi kira ga Pakistan ta hada gwiwa da gwamnatinsa domin yaki da ta'addanci.

Shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani, ya yi gargadin cewa idan har ba a fara tattaunawar neman zaman lafiya da kungiyar Taliban zuwa watan Afrilu ba, rikice-rikice za su ta'azzara a yankinsu.

Shugaban ya kuma ce illar da hakan zai haifar shi ne, ko wace kasa a yankin za ta ji a jikinta.

Da yake magana da BBC, Shugaba Ashraf Ghani ya yi kira ga Pakistan da ta hada hannu da gwamnatin kasarsa wajen yaki da ta'addanci.

Ya ce 'yan ta'addan da sojojin Pakistan suka kora har suka tsallaka iyaka, kasashen biyu suke neman far ma wa.

Shugaba Ghani ya kuma yi kiran a hada karfi da karfe, a yaki kungiyar IS da 'ya'yan ta suke kara yawa a kasar sa.

Ya ce ba za mu sadaukar da makomarmu saboda ayyukan wasu ba. Kungiyar Da'esh ba ta da muhalli a Afghanistan, kuma akwai bukatar a kawar da ita.