An yi kiran sauya shugabannin ANC

Tutar ANC Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Fitaccen mai fafutikar nan na Afrika ta Kudu, Denis Goldberg, ya bukaci da a sauya shugabannin Jama'iyar ANC, mai mulkin kasar.

An yi wa Mr Goldberg shara'a tare da Nelson Mandela kuma ya kashe shekaru fiye da 20 a gidan yari.

Ya shedawa BBC cewar cin hanci yayi wa dukanin matakan shugabanci na ANC , daga kananan hukumomi zuwa na kasa katutu.

Ya ce mayar da hankalin da suka yi na azurta kai na hana wa 'yan Afrika ta Kudu 'yancinsu.