Brazil: Zamu dau mataki kan Zika saboda Olympic

Wani yaro da ya kamu da kwayar cutar Zika a Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani yaro da ya kamu da kwayar cutar Zika a Brazil

Hukumomi a Brazil sun sanar da daukar matakan na kare yaduwar kwayar cutar Zika a lokacin wasan Olympics da za a yi cikin wannan shekarar.

Barkewar cutar ta Zika sakamakon cizon sauro, wacce ke sa ana haihuwar jarirai da tawaya, ya sa mutane a kasar ci gaba da nuna fargaba.

Jami'ai a kasar, a kokarinsu na kwantar da hankalin miliyoyin mutane da zasu isa birnin Rio domin wasannin, sun ce tun watannin hudu kafin a fara wasannin, za a fara duba wuraren wasannin don ganin sauro bai basu wurin zama ba.

Sannan kuma, jami'an suka ce za a rika share wuraren wasannin a kullun idan aka fara tsalle-tsallen.

Jami'an suka ce za a yi taka tsantsan wajen yin feshin maganin sauro a lokacin wasannin saboda kare lafiyar 'yan wasa da kuma 'yan kallo.