Bam ya hallaka mutane 25 a Kamaru

Rahotanni daga Kamaru sun ce wasu 'yan mata 'yan kunar-bakin-wake sun tayar da bama-bamai uku a garin Bodo, da ke kusa da kan iyaka da Najeriya.

An tashi biyu daga cikin bama-baman ne dai a kasuwar garin, wacce ke cike makil da jama'a.

Jami'ai sun ce an kashe a kalla mutane 25 galibinsu a harin da aka kai a kasuwa.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da kai wadannan hare-haren, kuma a baya mayakan kungiyar sun hallaka mutane da dama a Bodo.

Wani mazaunin garin na Bodo ya yi wa Muhammad Kabir Muhammad karin bayani ta wayar tarho

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti