CAR: Kotu ta soke zaben 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto
Image caption A mako mai zuwa za a je zagaye na biyu na zaben shugaban kasa

Kotun tsarin mulki a jamhuriyar tsakiyar Afirka ta soke sakamakon zaben majalisar dokokin da aka gudanar a watan da ya wuce.

A cewarta, akwai kura-kurai da yawa a zaben.

To amma kotun ta tabbatar cewa, tsofaffin Firai ministan kasar biyu: Anicet Dologuele da Faustin Touadera, su ne za su yi takara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, wanda za a yi a makon gobe.

Dubban jama'a ne suka hallaka a shekaru ukun da suka wuce, a rikicin da ya barke a jamhuriyar tsakiyar Afirkar.