Anya Donald Trump ba zai zama shugaban Amurka ba?

Hakkin mallakar hoto Getty images

Jam'iyyar Republican ta Amurka ta fada cikin halin gaba kura baua sayaki a daidai lokacin da take shirin zaben mutumin da zai yi mata takarar shugabancin kasar a taron da wakilanta za su yi a jihar Iowa.

Mutanen da ke son yin takara a karkashin jam'iyyar, wadanda ke da saukin-kai irinsu Marco Rubio,da Jeb Bush, da John Kasich da Chris Christie - ba sa cikin wadanda ke da farin jini a wajen 'yan jam'iyyar.

Da wuya ka kalli daya daga cikinsu, sannan ka kwatanta shi da Donald Trump daTed Cruz, wadanda ke da matukar tsattsaura ra'ayi da kuma janyo wa jam'iyyar cece-kuce.

Kuma a maimakon wadanda ke da sauki-kan su hada kawuansu su kuma fuskanci Trump ko Cruz, da alama sun bige da yi wa kansu bi-ta-da-kullin-siyasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Don haka ko da ya ke masu ruwa-da-tsaki a jam'iyyar sun amince cewa tsayar da Mista Trump ba karamar kasada ba ce, da alama samun wanda zai kayar da shi ba karamin aiki ba ne.

Sun kuma amince cewa za su iya tsayar da Mista Trump , amma ba za su iya tsayar da Mista Cruz a matsayin dan takara ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Mista Trump mutum ne da kan amince da ra'ayoyin da ba irin nasa ba, amma Mista Cruz ba ya karbar shawarwari.

Don haka za a iya cewa jam'iyyar ta Republican za ta yi abin da Hausawa kan ce "da rashin uwa a kan yi uwar daki".

Wani abu da kowa ya amince da shi shi ne, Donald Trump ne zai yi wa jam'iyyar takara a zaben shekarar 2016, sai dai idan wani abin al'ajabi ne ya faru.

Kuma idan Mista Trump ya zama shugaban kasar Amurka, to shi ne mutum na farko da zai rike mukamin ba tare da ya taba rike wani mukamin siyasa ko na soja ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani tsohon dan jam'iyyar, Sanata Bob Dole, mai shekara 92, wanda kuma tsohon dan takarar shugabancin kasar ne, ya ce idan aka tsayar da Mista Cruz, wanda dan majalisar dattawa ne daga jihar Texas, "jam'iyyar za ta fuskanci wani abu mai kama da girgizar kasa".

Shi ma Terry Branstad, gwamnan jihar Iowa, ya ce bai ga dalilin da zai sa a tsayar da Ted Cruz takara ba.

A baya bayan nan ne dai Sarah Palin ta bayyana goyon bayanta ga Mista Trump.

Don haka za a iya cewa Mista Trump ba zai yi nasarar yin takara a karkashin jam'iyyar ba ne kawai idan jihohin Iowa daNew Hampshire - wadanda su ne za su fara kada kuri'unsu da kuma masu ruwa-da-tsaki a jam'iyyar -- suka amince su samu wani dan takarar da zai maye gurbin Mista Trump.