Jami'an tsaron Masar suna shirin ko-ta-kwana

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Masu zanga zanga a Masar

An baza jami'an tsaro a manyan biranen Masar domin hana mutane zanga-zangar cika shekara biyar da juyin-juya-halin da ya hambarar da Shugaba Hosni Mubarak.

Jami'an tsaron sun fi mayar da hankali ne ga dandalin Tahrir, wurin da aka fi yin zanga-zanga a lokacin juyin-juya-halin.

A 'yan kwanakin da suka gabata, jami'an tsaro a Masar din sun kai samame a gidaje kimanin dubu biyar a Alkahira, babban birnin kasar, a wani yunkuri da hukumomin kasar ke farautar mutanen da ke shirin yin zanga-zanga a ranar Litinitin din nan.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce take hakkin dan adam da ake yi a Masar din yanzu, ya fi na kowanne lokaci muni.

Kungiyar ta ce Masar -- a karkashin shugaba Abdel Fata Alsisi ta koma kama-karya -- lamarin da ya sa fatan da jama'a suka yi lokacin juyin-juya-halin ya-bi-ruwa.

Shekaru biyar da juyin-juya-hali da ya hambarar da Hosni Mubarak daga mulki, 'yan tsirarun abubuwa ne kawai suka rage da suke sa wa ake tunawa da juyin-juya-halin.