Kasuwar wayar iPhone na tangal-tangal

Wayar iPhone Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A farkon fitowar wayar ta yi matukar farin jini tsakanin matasa.

Kamfanin Apple ya ba da sanarwar cewa kasuwarsa ta fadi ta fuskar sayar da wayar iphone a karshen shekarar 2015, sakamakon koma-bayan tattalin arzikin da kasar China ke fuskanta.

Kamfanin dai ya sayar da wayar iphone miliyan 75 ne a cikin watanni uku na karshen shekarar da ta gabata, kuma a halin da ake ciki, cinikin wayar ya yi raguwar da bai taba yin irin ta ba, tun lokacin da aka kaddamar da wayar a shekara ta 2007.

Sai dai ribar kamfanin ta karu da sama da dala biliyan 18.

A cikin watanni masu zuwa Kamfanin Apple zai mayar da hankali ne wajen nazarin raguwar da kudin-shigarsa ke yi da gaggawa, tun daga lokacin da aka kaddamar da wayar iphone.

Kasuwar wayar ta kai makura, don haka wajibi ne kamfanin ya fara tunanin wayar da zai kera da za ta maye gurbin iphone.