Boko Haram: An kama Basarake a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro na shirin kota-kwana a Kamaru

Hukumomin tsaro a Kamaru sun tsare wani basaraken gargajiya a yankin Logone et Chari da ke Lardin arewacin kasar bisa dililan tsaro.

Jami'an tsaro na bataliya ta 41 ne suka kama hakimin Kolafata, Malam Brahim Djakari a ci gaba da wani bincike kan ayyukan Boko Haram a yankin.

Baya ga wannan Hakimin akwai kuma wasu mutane biyar da aka tsare tare da shi.

Bayanai sun ce a karo da dama, an dinga ambatar sunan wannan hakimi a cikin wasu harkoki masu alaka da ta'addancin da kungiyar Boko Haram take haddasawa.

Kawo yanzu babu wani martani a daga bangaren hakimin.

Jami'an tsaron Kamaru na daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kasashen tafkin Chadi da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

Bayanai sun ce yan kungiyar Boko Haram sun kashe kimanin mutane 1,200 a Kamaru tun daga shekarar ta 2013.