Gobara ta lalata kasuwar 'Railway' a Kaduna

Image caption 'Yan kasuwar sun tafka hasara sosai

Gobara ta lalata daruruwan shaguna a kasuwar 'Railway' da ke kusa da unguwar Barnawa a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Bayanai sun ce matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar wacce ta shafe sa'o'i tana ci, lamarin da ya janyo hasarar dukiya ta miliyoyin Naira.

Kasuwar ta yi suna wajen samun kayan abinci kamar shinkafa da doya da wake da sauransu.

'Yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar amma duk da haka ta lalata galibin shagunan kasuwar.

Yawancin shagunan kasuwar na katako ne da kwano abin da ake ganin shi ne ya kara rura wutar da ta tashi.

Bayanai sun ce gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ziyarci kasuwar domin ganin irin barnar da ta wutar ta haddasa.

Ga hotunan da wakilinmu na Kaduna, Nurah Mohammed Ringim ya aiko mana