Kananzir ya zama gwal a Nigeria

Layin Mai a Nigeria
Image caption Matsala karancin Man Fetur da Kananzir na ci gaba da ciwa 'yan Nigeria tuwo a kwarya.

'Yan Nigeria suna ci gaba da mayar da martani kan karin farashin kananzir da gwamnatin kasar ta yi.

A wannan makon ne dai gwamnatin Najeriyar ta sanar da karin Naira 33 a kan kowace lita, ma'ana ta tashi daga Naira 50 zuwa naira 83.

Alhaji Bashir Dan Malam shi ne shugaban kungiyar masu gidajen Mai masu zaman kansu wato IPMAN a jihar Kano, ya shaidawa BBC cewa karin farashin ba shi da wata illa matukar za a samar da shi a duk fadin kasar.

To sai dai Alhaji Lawal Muhammad Dan Zaki na kungiyar ta IPMAN na ganin karin bashi da wata fa'ida, idan aka yi la'akkari da karin da aka dade ana yi a kan man Fetur da shi Kananzir, amma har yanzu bai wadata a kasar ba.