Kotu ta wanke Firai ministan Malaysia

Gwamnatin Malaysia ta ce an mayar wa Saudiyya kudin da ta ba Najib Razak.
Bayanan hoto,

Gwamnatin Malaysia ta ce an mayar wa Saudiyya kudin da ta ba Najib Razak.

Gwamnatin Malaysia ta wanke Firai ministan kasar Najib Razak daga zargin karbar cin hanci.

Ana zargin Mista Razak ne dai da hannu a wata badakalar karbar hanci da ke da alaka da asusun zuba jari na kasar

Sai dai wata sanarwa da ofishin babban lauyan gwamnatin kasar ya fitar ya ce kasar Saudiyya ce ta bai wa Mista Razak kyautar dala miliyan 681 da aka gani a asusunsa.

Kudaden, wadanda a baya aka ki yin bayani a kan su, sun janyo wata badakala ta wata da watanni a siyasar Malaysia.

A halin yanzu, babban lauyan gwamnatin Malaysia, Mohamed Apandi Ali ya ce ya gamsu babu wani laifi da Mista Razak ya aikata.

Sai dai ya ce Saudiyya ba ta bayar da wani dalili na yi wa Firayi ministan kyautar kudin ba, yana mai cewa an mayar wa kasar akasarin kudaden.