Editocin Wikipedia sun yanke-kauna ga hukumar gudanarwarsu

Image caption wikimedia

Sama da editocin shafin nan na komai-da-ruwanka, mai samar da bayanai ta intanet, wato Wikipedia su 200 sun yanke-kauna ga da mambobin hukumar gudanarwar da aka nada musu.

A wannan watan ne aka nada Arnnon Geshuri, wanda tsohon manaja ne a kamfanin Google a matsayin mamba a gidauniyar Wikimedia.

Editocin dai na adawa ne da nadin da aka yi masa, saboda acewarsu ana zarginsa da hannu a wata farautar dabbobi da aka haramta.

A watan Janairun da ya wuce kamfanin Apple da Google da Intel da kuma Adobe suka biya wani kudi da ya kai dala miliyon 415 sakamakon wata karar da aka shigar kotu mai alaka da wannan zargi da Editocin ke yi.

Daya daga cikin Editocin ya ce mamaki ya kama su dangane da nadin da aka yi wa Mr Geshuri a matsayin mamban kwamitin aimintattu.

Ya ce "mamaki ya kama ni. Mene ne ya sa za a zabi irin wannan mutumin, mai irin wannan shaidar?"

wani Editan kuma cewa ya yi "na yanke-kauna game da wannan hukumar gudanarwa baki daya. Wannan lamari yana nuna kwamitin da wata siffa mai muni."

Sai dai wasu editoci 20 sun goyi bayan nadin da aka yi wa mambobin kwamitin amintattun.

Editocin da ke sukar nadin sun tura korafin nasu ne da wata sanarwa wadda ta ce tuni Editocin suka tura wata budaddiyar wasika zuwa ga shugaban hukumar gudanarwar Wikimedia.