Iyayen dalibai na korafin jarrabawa a Borno

Daliban Makaranta a Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na ganin cewa gwamnatoci ba sa mai da hankali ga bunkasa ilimi a Nigeria

A Jihar Borno da ke arewacin Najeriya iyayen daliban sakandare na korafi kan batun da ya shafi jarrabawar kammala makarantun sakandare wato WAEC da NECO na 'ya'yansu.

Iyayen sun koka kan rashin biyan kudaden jarrabawar daga gwamnatin jihar, lamarin da yasa har yanzu yaran suka kasa samun shiga Jami'oi da manyan Kwalejoji.

Kimanin shekaru biyu kenan da rufe makarantun sakandare a jihar Bornon, sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

Sai dai gwamnatin jihar Bornon a nata bangaren, ta ce ta biya kudaden jarrabawar, kuma ana gab da ba wa daliban sakamakonsu.