Facebook ya samu tagomashi a bara

Facebook Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shafin sada zumunta na Facebook na da matukar farin jini tsakanin matasa.

Kamfanin nan mai shafin sada zumunta ta Intanet, wato Facebook ya ce kudin-shigarsa ya karu da sama da kashi 50 bisa dari a karshen shekarar da ta wuce idan aka kwatanta da bariya.

Kamfanin ya bayyana cewa ya samu dala biliyon biyar da miliyon dari takwas a tsakanin lokacin da ake magana.

Ya kuma ce a kowace shekara masu na amfani da shafin na karuwa da kashi 14 bisa dari, wato kusan mutum biliyon daya da miliyon dari shida a cikin wata guda.

A cewar kamfanin Facebook din, yanzu ma'abota shafin da dama na amfani da wayoyinsu ne wajen shiga shafin, kuma sun kai kashi ashirin da daya bisa dari a kowace shekara, inda suke samar da kashi 80 bisa dari na kudin da kamfanin ke samu ta fuskar tallace-tallace.