Ministar Shari'a ta yi murabus a Faransa

Image caption A ranar Alhamis ne Firai Minista, Manuel Valls zai gabatar da sauye-sauyen ga majalisa

Ministar shari'a ta kasar Faransa, Christiane Taubira ta yi murabus daga mukaminta kan cece-kucen da ake yi na soke takardar izinin zama 'yan kasa ga duk wanda aka kama da laifin ta'addanci.

Shawarar yin hakan na daga cikin matakan da ake son dauka bayan harin da masu ikirarin kishin Musulunci suka kai a Paris a watan Nuwamba.

Wakilin BBC a Paris ya ce batun ya janyo muhawara mai zafi kan yiwuwar aiwatar da matakin ko rashin yiwuwarsa.

Kuma ko zai shafi mutanen da ke da takardun zama 'yan kasa na wasu kasashen.