Netanyahu da Ban Ki Moon suna cacar-baki

Image caption Ban Ki Moon ya ce Isra'ila ba ta da hujjar ci gaba da mamaye Palasdinawa.

Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya zargi Sakataren Majalisar Dinkin duniyar, Ban Ki Moon, da iza-wutar ta'addanci, sakamakon furucin da ya yi cewa martanin da Palasdinawa ke mayarwa dangane da mamayar da ake musu dabi'a ce ta Dan adam.

A wani jawabin da ya yi ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, Mista Ban Ki Moon ya soki shirin Isra'ila na yin wasu sababbin gine-gine a gabar Kogin Jordan, yana cewa tsokana ce zalla da ke sanya shakku game da dukufar Isra'ilar wajen daidaitawa ta hanyar ba wa Palasdinu matsayin cikakkiyar kasa.

Sakataren Majalisar Dinkin duniyar ya yi tir da hare-haren da ake kaiwa kan Yahudawa, yana cewa daukan matakan tsaro tsingaliminsu ba zai magance rikicin da ake fama da shi a yankin ba.

Ya ce dole sai doka ta yi aiki a kan dukkan masu aikata miyagun laifuka ta hanyar kamanta adalci daidai-wa-daidai a kan Yahudawa da Palasdinawa.

Amma, Mista Netanyahu a nasa raddin, ya ce Majalisar Dinkin duniya ta dade da barin matsayinta na mai tsayawa a tsakani, ta koma karkata ga wani bangare guda.