Ana yunkurin sasanta tsakanin Musulmai da Kirista

Kungiyar Jama'atul Nasrul Islam tare da hadin gwiwar majalisar Kiristoci ta Najeriya, sun kafa wata cibiya ta hadaka domin shiga tsakani da sasantawa a kokarin magance rikice-rikicen addini da ya addabi kasar.

Shugabannin wannan cibiya wadda suka ce ta din-din-din ce na da zummar kara samar da hadin-kai tsakanin Kiristoci da kuma Musulman kasar, tare da ba da sahihan bayanai a kan al'amurran da suka shafi mabiya addinan biyu.

To ko ina wannan cibiya ta sha banban da saura da aka kafa a baya?

Ga dai rahoton da wakilinmu Nurah Mohammed Ringim ya aiko mana daga Kaduna.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti