Ukehe:'Gari na masu tsawon rai a Enugu'

Hakkin mallakar hoto BBC ABDUSSALAM AHMED

Garin Ukehe na jihar Enugu a kudu maso gabashin Najeriya, kamar kowanne gari ne na duniya.

Sai dai abin da ya bambanta shi da sauran garuruwa, shi ne yadda akan sami mutane masu tsawon rai, wadanda shekarunsu a duniya kan haura dari.

Ba da dadewa ba ne ma wani dattijo ya rasu yana da shekaru dari da hamsin, kuma wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya sami zantawa da wasu tsofaffin, daya mai shekaru da dari da talatin da biyu, daya kuma dari da ashirin.

Hakkin mallakar hoto BBC ABDUSSALAM I AHMED
Image caption Cif Ugwu ya ce shekarunsa 132

Ba wai baiwar kasar noma da itatuwan da kan samar da kudi garin Ukehe na jihar Enugu yake da ita kadai ba, garin yana kuma da baiwar mutane masu tsawon rai.

'Sa'o'ina sun mutu'

Cif David Ugwu na kauyen Amadim, mai shekaru dari da talatin da biyu a duniya, kamar yadda takardar shaidar baftismarsa ta coci ta nuna.

"Sa'o'ina duka sun mutu, ba sauran wadanda muka yayi tare, ballantana in ganinsu. Daga nan har zuwa garin Nsukka duk na san sa'o'ina, amma babu sauransu," in ji Ugwu.

Hakkin mallakar hoto BBC ABDUSSALAM I AHMED
Image caption Ba ni da sauran abokai a raye

Ya kara da cewar "Na yi aiki a matsayin akawu, mun yi aikin karbar wa gwamnati haraji. Na kuma taba harkar kasuwanci, inda na rika zuwa ina saro busasshen kifi da taba in sayarwa can shekarun baya."

Ko da na tambayi dattijon irin abincin da ya fi sha'awa a yanzu, sai ya kada baki ya ce "Kai ma dai wannan mutum, ai duk wani abinci mai dadi ina shawarsa, ba ma kamar doya da abincin da aka yi daga rogo da shinkafa da dai sauransu."

'Kauyen Nkporogwu'

A kauyen Nkporogwu na garin na Ukehe, can ma akwai wata dattijiyar mai suna Okpuechi Iyizeze, wadda aka ce tana da shekaru dari da ashirin a duniya.

"Na dade a duniya, har ma ba san iya shekaruna ba, duk sa'o'ina sun rasu, kuma a yanzu ina da'ya'ya bakwai da jikoki da tattaba kunne da dama," in ji Iyizeze da harshen Ibo.

Hakkin mallakar hoto BBC ABDUSSLAM I AHMED
Image caption Mama Iyizeze ta na rayuwarta a kauye

Tsofaffin biyu dai suna da abubuwa da dama iri daya, domin baya ga yin amfani da sanda a zirga-zirgar da sukan yi a yau da kullum a cikin gida, da kansu suke cin abinci, da zagayawa ban-daki, da yin wanka, duk dai karkashin kulawar iyalansu.

Kowannensu kuma yana cikin hayyacinsa, ko da yake sukan yi fama da matsalar mantuwa jefi-jefi.

'Ta bakin basaraken Ukehe'

Igwe Emmanuel Aruah, basaraken gargajiya na garin Ukehe, ya ce tsawon rai wani abu ne da aka saba da shi a garin tun shekaru aru-aru.

"A gaskiya ma dai kakannin-kakanninmu sun yi shekaru dari biyu a duniya, wasu ma fiye da haka. Don haka mukan yi tsawon rai fiye da wadannan na yanzu," in ji Igwe Aruah.

Hakkin mallakar hoto BBC ABDUSSALAM I AHMED
Image caption Babu kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin wannan dattijiyar game da shekarunta

Aruah ya kara da cewa "Hakan kuwa yana da nasaba da tsarin rayuwarmu mai cike da tsoron Allah, da rashin tashin hankali, da wadatar zuci da dai sauransu."

Basaraken gargajiyan ya kara da cewa sukan yi amfani da hanyoyi daban-daban, wajen tantance shekarun mutane masu tsawon rai, kamar rubutu da tarihin aukuwar wani abu ko wasu bukukuwa na gargajiya.