Greg Dyke: Shugaban FA zai bar mukaminsa

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban FA Greg Dyke zai bar mukaminsa bayan shekaru 3

Greg Dyke ba zai sake tsayawa zabe ba a matsayin shugaban FA idan wa'adin da ya ke ciki ya kare a watan Yuni

Dyke wanda aka nada a shekarar 2013, ya ce zai sake tsayawa takara

Sai dai a ranar Alhamis ya bayyana cewa adawar da ake na wasu sauye saauye da wasu jami'an hukumar FA da kuma tsirarun mambobin hukumar suka gabatar ya sa ya canza shawara.

Dyke ya ce kamata ya yi Ingila ta yi harin kai wa wasan kusa da na karshe a Euro 2020 sannan kuma ta lashe kofin duniya a shekarar 2022 idan ya karbi aiki daga David Bernstein