Fyade: An bude makarantar Hassan Gwarzo

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje
Image caption Tun da fari hukumomin makarantar sun musanta zargin fyaden

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun bayar da umarnin sake bude makarantar sakandare ta Hassan gwarzo, wacce ake zargin wasu dalibanta da yin luwadi.

An rufe makarantar ne a watan Oktoban bara, bayan zargin cewa an yi lalata da wasu dalibai.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammed Garba, ya shaida wa BBC cewa, an yanke shawarar sake bude makarantar ce bayan nazarin rahoton bincike da aka mika mata.

Rahoton kwamitin dai ya gano cewa babu wata shaida kwakkwara da ke nuna an yi lalata da daliban, ko da yake akwai alamun an yi yunkurin hakan.

Kazalika, rahoton ya bai wa hukumomin makarantar shawarar cewa su dinga sanya ido a mu'amalar dalibai, musamman a dakunan kwanansu.