Iran ta kulla yarjejeniya da Peugeot

Hakkin mallakar hoto FARS
Image caption Kamfanin Peugeot babban kamfani ne a Faransa

Kasar Iran ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da kamfanin kera motocin Peugeot domin ya rika kera motocin a kasar ta Iran.

An sanar da wannan shiri ne a lokacin ziyarar da Shugaban Iran Hassan Rouhani ke yi a birnin, inda yake son farfado da dangantakar kasuwanci da ke tsakanin kasarsa da Turai.

Ana sa ran Mr Rohani zai kuma sanya hannu kan wata yarjejeniya, inda kamfanin Airbus zai kerawa Iran jirage fiye da dari daya.

A lokacin da ake bikin yi masa maraba da zuwa Paris, Mr Rouhani da ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, sun tsaya kyam yayin da dakarun sojin Faransa ke rera taken kasar ta Iran.

Idan anjima kada ne ake sa ran Mr Rouhani zai gana da shugaban Faransa Francois Hollande, sannan ya tattauna da jami'an wasu manyan kamfanonin Faransa.

An dai cire takunkumin da kasashen duniya suka sanyawa Iran, bayan ta amince ta janye shirinta na kera makamashin nukiliya.