Saraki ya mayar wa Obasanjo martani

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obasanjo ya saba rubuta wasika ga shugabanni a Nigeria

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Abubakar Bukola Saraki ya mayar da martani ga tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo, kan batun wasikar da ya aika majalisun dokokin kasar.

A cikin wasikar, Obasanjo ya zargi 'yan majalisar dokoki da cin hanci da kuma almubazzaranci da dukiyar kasa duk da irin mummunan yanayin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

Obasanjo ya zargi sanatoci da 'yan majalisar wakilai da tsara wa kansu albashi da alawus-alawus fiye da abin da hukumar tara kudin shiga da raba shi da kuma tsara albashi da hakkokin ma'aikata ta kasa (RMAFC), ta kayyadewa 'yan majalisar.

A martaninsa ta shafinsa na Twitter, Saraki ya godewa tsohon shugaba Obasanjo, sannan kuma ya jaddada cewa majalisun dokokin kasar karkashin jagorancinsa, na mayar da hankali wajen shugabanci nagari da adalci da kuma yin aiki a bayyane ta yin la'akari da yanayin tattalin arzikin kasar.

Saraki ya kara da cewa a yanzu majalisar ta bullo da wasu sauye-sauye kan yadda ake kashe kudin majalisun dokokin kasar.

Ga rahoton da Haruna Shehu Tangaza ya hada mana kan batun.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti