'Yan Somalia na zanga-zangar adawa da Al-Shabab

Image caption An kashe mutane kimanin 20 a wannan hari.

Daruruwan 'yan Somaliya sun tafi bakin tekun da aka kai wani hari don nuna adawarsu kan irin abin da mayakan Al-Shabab ke yi a kasar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne mayakan suka kai hari bakin tekun wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 20, bayan da bam ya tashi a cikin wata mota sannan kuma suka bude wuta a wani kantin cin abinci da bakin tekun na Lido.

An gina wuraren cin abinci da kantunan shan shayi da otal-otal da dama a yankin, tun bayan da aka kore mayakan Al-Shabab daga birnin shekaru biyar da suka gabata.

Kungiyar ta ce ta kai hari kantunan cin abincin da ke bakin tekun ne saboda mafi yawa jami'an gwamnati ne suke ziyartar wajen.