An yi kisan gilla a Burundi - Amnesty

Image caption Tun bayan da shugaban Burundi ya yi tazarce ake ta fama da rikici a kasar.

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta Amnesty International, ta ce ta ga wasu sababbin hotuna ta tauraron dan adam da ke nuna cewa an kashe 'yan Burundi da dama, an kuma binne su a cikin manyan kaburbura.

Kungiyar Amnesty ta ce hotunan na nuna wasu wurare masu alamun manyan kaburbura guda biyar a yankin Buringa da ke wajen Bujumbura, babban birnin kasar.

A cewar kungiyar, cikin hotunan har da bayanai daga wasu mutane da lamarin ya auku a kan idanunsu, wadanda suka ce an dai tona kaburburan ne a watan Disambar bara.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan wani rikici da aka yi a Burundin, inda aka kashe a kalla mutune 87, lokacin da shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da cewa zai yi ta-zarce.