Faransa ta bukaci Burundi ta saki 'yan jarida

Image caption An dau tsawon lokaci ana rikici a Burundi.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi kira ga hukumomin Burundi da su yi gaggawar sakin wasu 'yan jarida biyu na kasashen ketare, wanda dayansu Bafaranshe ne.

'Yan sanda ne suka kama 'yan jaridar da Bafaranshe Jean Philippe Remy da kuma wani mai daukar hoto dan Biritaniya Phil Moore da sauran wasu mutane 15 a wata unguwar 'yan adawa a Bujumbura, babban birnin kasar.

'Yan jaridar wadanda suka karbi lambobin yabo da dama dangane da aikinsu, sun sha zuwa Burundi tun lokacin da aka fara rikici a kasar.

Kungiyar 'yan jarida 'yan kasashen waje ta Gabashin Afrika ta ce ta damu matuka da kama abokan aikinta da aka yi wadanda ta bayyana da cewa fitattun 'yan jarida ne.

Daruruwan mutane sun rasu a kasar Burundi, saboda batun tazarcen shugaba Pierre Nkurunziza.