Shin ko laifi ne kawar da sauro baki daya?

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption An kasa nau'in saurayen da ke yada cuta ga bil'adama zuwa uku

Sauro wata halitta ce da ke da matukar hadari a duniya, domin yana yada cutar da ke kashe mutane miliyan daya a duk shekara.

A halin yanzu kuma ga cutar Zika da sauro ya ke yadawa, wanda aka alakanta da haihuwar dubban jariran da ke da nakasa a kwakwalwarsu a kudancin Amurka.

To ko laifi ne idan aka ce za a kawo karshen sauro a duniya?

Akwai nau'in sauraye har 3,500, sai dai mafi yawansu basu da illa ga dan Adam, domin suna rayuwa ne a kan tsirrai da 'ya'yan itatuwa.

Amma mata cikin sauraye kashi shida cikin darin da ake da su ne ke shan jinin bil'adama, wanda ke taimaka musu wajen yin kwai. Kuma kimanin rabin wadannan matan ne ke dauke da kwayoyin cutar da ke cutar da mutane. Saidai bala'in da sauro kala 100 ke janyo wa na da girman gaske.

Frances Hawkes na cibiyar albarkatun kasa da ke jami'ar Greenwich ya ce "Rabin mutanen duniya na cikin hadarin kamuwa da cututtukan da sauro ke yadawa" Ya kara da cewa "Sun janyo tashin hankali ba karami ba ga bil'Adama.

Fiye da mutane miliyan daya wadanda mafi yawansu sun fito daga kasashe matalauta ne ke mutuwa da cututtukan da sauro ke yadawa da suka hada da zazzabin Maleriya da cutar Zika da cutar shawara da zazzabin dengue.

Haka kuma wasu saurayen na yada cutar Zika wanda da fari an yi tsammanin yana janyo zazzabi ne kawai da kuraje.

Amma a yanzu masana kimiyya na nuna damuwa cewa cutar kan haddasa nakasa ga jariran da ke ciki.

Ita dai cutar Zika ana dangantata da haihuwar jarirai masu karamin kai a kasar Brazil.

An yi ta kokarin wayar wa da mutane kai cewa su yi ta amfani da gidan sauro mai feshin magani da wasu hanyoyi na kaucewa cizon sauro.

Hakkin mallakar hoto Getty

Amma ba zai fi sauki ba kawai ace an shafe sauraye daga doran kasa?

Wata masaniya a fannin kimiyya Olivia Judson, ta gaya wa jaridar New York Times cewa, kashe nau'in sauraye 30 ta hanyar sanya musu maganin kashe kwari zai kare mutane miliyan daya, kuma ya rage yawan nau'oin saurayen da ake da su da kashi daya cikin dari.

Wani kwararre a kan ilimin kwari na jami'ar Florida Phil Lounibos, na ganin "Kawar da sauro daga doron kasa zai haifar da matsaloli da dama."

Ya yi nuni da cewa saurayen da suka dogara a kan tsirrai suna da amfani wajen yabanyar tsirran, kuma su ne abincin tsuntsaye da jemagu, yayin da kifaye da kwadi ma ke cinsu kafin su yi fuffuke.

Saboda haka kashe wadannan sauraye zai janyo gibin abincin wasu kwari.

Sai dai kan hakan wasu masanan na ganin cewa wasu kwari za su maye gurbin saurayen.

Shi ma Jonathan Pugh na jami'ar Oxford na Ingila na ganin ba dace ba a kawar da wani nau'in sauro baki daya.

Hakkin mallakar hoto Getty

Sai dai a yunkurin neman bakin zaren, wasu masana a Amurka sun fara kiwon wasu saurayen da aka sauya halittarsu ta yadda za su bijirewa kwayoyin cutar Maleriya.

Ko da yake tuni wasu masana a jami'ar Oxford na Burtaniya suka sauya halittar wasu nau'in saurayen da ke dauke da kwayar cutar Zika ta yadda 'ya'yan da suka haifa za su mutu da wuri kafin su girma su yada cutar.

An watsa irin wadannan saurayen miliyan uku a wani wuri a tsibiran Cayman a shekarar 2009 zuwa 2010 iya yada cutar ba.

Kuma an samu raguwar saurayen da kashi 96 cikin dari idan aka kwatanta da sauran wurare.

Haka kuma wani gwajin da ake yi a halin yanzu a Brazil ya kai ga rage kashi 92 cikin dari na saurayen.